A can wata Kasa an haifi wani jinjiri da kafafu guda hudu

A can wata Kasa an haifi wani jinjiri da kafafu guda hudu

- An ga abin mamaki a kasar Mozambique yayin da wata mata ta haifi wani jariri mai kafafu barkatai

- An haifi wannan jinjiri da kafafu har guda hudu

- Wannan abu ya faru ne a yammacin kasar Mozambique

A can wata Kasa an haifi wani jinjiri da kafafu guda hudu

 

 

 

 

 

A Kasar Mozambique wani abin al’aji ya faru, inda aka haifi wani jinjiri da kafafu har guda hudu a jikin sa. A cewar Jaridar Magazine Independete ta Kasar, yanzu haka likitoci na kokarin aiki a kan yaron.

Likitocin Asibitin na kokarin ganin sun yi iya bakin kokarin su wajen ceto wannan yaro. Ko da yake dai har yanzu ba a bayyana jinsin jinjirin ko fito da ainihin hoton sa ba, likitoci na shirin yi masa aiki.

KU KARANTA: An dakatar da Sallah a Masallacin Sultan Bello

Wannan abin mamaki dai ya faru ne a Yankin Manica da ke Yammacin Kasar na Mozambique. Jaridar Magazine Independete-da ake rubutawa da harshen Kasar Portugal ta bayyana cewa mahaifyar wannan yaron ta dauki ciki kana ta haihu lafiya lau ba tare da wata matsala ba.

Sai ga shi an haifi wannan yaro da kafafu guda hudu a jikin sa, sai dai ba yau aka fara samu irin wannan ba. Ko a shekarar nan an haifi wani yaro da kafafu uku a wannan Gari na Manica.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel