Wani mutumin Goodluck Jonathan, Henry Ogiri ya koma APC

Wani mutumin Goodluck Jonathan, Henry Ogiri ya koma APC

- Wani na kusa da Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tsere daga Jam’iyyar PDP

- Henry Ogiri ya koma Jam’iyyar APC mai mulkin Kasar

- Ogiri Darektan NDDC ne lokacin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan

Wani mutumin Goodluck Jonathan, Henry Ogiri ya koma APC

 

 

 

 

 

 

 

Dr. Henry Ogiri, wani tsohon Darektan kudi a Ma’aikatar NDDC na Neja-Delta ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa ta APC mai mulki. Dr. Ogiri wanda dan Jihar Rivers ne ya bayyana sauyin shekar na sa ne a karshen wannan makon.

Tsohon Darektan ya tabbatar da tashin sa daga Jam’iyyar PDP mai mulkin Jihar zuwa APC a wani taron gangami na Jam’iyyar APC din da aka yi a yankin Abua na Karamar Hukumar Abua/Odua. An yi wannan taro ne a Ranar Asabar dinnan da ta wuce.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kori Abba Kyari?

Henry Ogiri aminin Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ne, yace ya shigo APC ne domin tafiya tare da Shugaba Buhari. Henry Ogiri yace Shugaba Buhari na da shirin gyara Najeriya, don haka ya kira magoya bayan sa da su shiga APC domin ayi wannan tafiya tare da su.

Rotimi Amaechi, jigon Jam’iyyar APC a karin, ko da bai samu zuwa taron ba, wani tsohon Sanata watau Magnus Abe ya wakilce sa a taron. Yace kowa ya san Dr. Ogiri mutumin kirki ne, ya tsaya ne a Jam’iyyar PDP dama don Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan. ‘Yan Jam’iyyar APC din sun soki Gwamnatin Jihar na PDP, sun ce yanzu Jihar ta shiga giyan baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel