Abin da ya sa ba zan taba Kwankwaso ba-Gwamna Ganduje

Abin da ya sa ba zan taba Kwankwaso ba-Gwamna Ganduje

- Gwamna Gaduje yace ba zai tsaya binciken Gwamnatin Kwankwaso ba

- Gwamna Ganduje yace zai maida hankali ne wajen yin ayyuka a jihar Kano

- Ganduje ne mataimakin Rabi’u Kwankwaso lokacin yana gwamna

Abin da ya sa ba zan taba Kwankwaso ba-Gwamna Ganduje

 

 

 

 

Gwamna Ganduje na jihar Kano yace ba zai tsaya bata lokacin sa ba wajen binciken gwamnatin Injiniya Rabi’u Kwankwaso. Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a Ranar Asabar dinnan, bayan taron Jam’iyyar APC na bangaren Kano da aka yi a Garin Sokoto.

Gwamna Ganduje yace duk da cewa mafi yawan Jihohi suna ta binciken abin da ya faru a Gwamnatocin baya, shi ba zai tsaya yin wannan ba. Gwamna Ganduje ne dai mataimakin Kwankwaso a lokacin yana Gwamnan Jihar Kano har sau biyu; a shekarar 1999-2003 da kuma 2011-2015.

KU KARANTA: Rahama Sadau a Amerika da su Akon

Gwamna Ganduje yace abin da zai karkata gare shi, shine ayyuka da tsare-tsaren da duk za su kawo cigaba a Jihar Kano. Gwamna Ganduje yace gwamnatin sa za tayi kokari karasa duk ayyukan kwarai da ta gada daga duk gwamnatocin baya wadanda za su kawo cigaba ga Jihar Kano.

Ana ta rikici tsakanin magoya Kwankwaso da shi Gwamna Ganduje, Gwamna Ganduje yayi tir da abin da ke faruwa, yace wasu ne kawai ke yada karya domin su ga bayan sa da gwamnatin sa. Gwamna Ganduje yace wannan abin Allah-wadai ne daga manyan ‘yan Kwankwasiyyan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel