Ana rikicin limanci a Masallacin Sultan Bello

Ana rikicin limanci a Masallacin Sultan Bello

Rikicin Limanci ya barke a Babban Masallacin nan na Sultan Bello da ke Kaduna

‘Yan Sanda sun harba bindiga ana tsakar Sallar Juma’a

An yi Sallar Jumu’a kashi biyu a Masallacin

Ana rikicin limanci a Masallacin Sultan Bello

Rikicin Limanci ya barke a Babban Masallacin nan na Sultan Bello da ke Kaduna. Abin har ta kai an katse Sallar Juma’a a Masallacin Jiya. Har dai sai da Jami’an tsaro suka shigo cikin lamarin gudun kar a saba doka.

Wani wanda a gaban sa aka yi komai ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa Na’ibin Limamin Masallacin ya gabatar da huduba kamar yadda aka saba, ya tashi ya fara bada Sallah, kwatsam kawai sa aka yi kokari a hana sa jan Sallar a Ra’aka ta farko, daga nan ne Jami’an ‘Yan Sanda suka shiga harbar bindiga da borkonon tsohuwa a cikin masallaci

KU KARANTA: Limamin Makkah zai zo Najeriya

Bayan Jami’an tsaro sun shiga harbi ne, sai kowa ya tsere daga Masallacin, daga nan kuma mutanen dayan Limamin watau Dr. Khalid suka shiga suka fara nasu Sallar Jumu’ar. Bayan dai sun fara kenan wasu matasa suka shigo Masallacin suka hana su Sallar, don dole suka tashi.

Jami’in ‘Yan Sanda ASP Aliyu Usman ya tabbatar da faruwar wannan rikici a Babban Masallaci na Sultan Bello. An dai jima ana Rikicin Limanci a Masallacin. Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya rubuta takarda a kwanaki yake bayanin abin da yake faruwa. Su dai ‘Yan Sanda sun ce rayuka suke karewa ba Liman suka nada ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel