Ubangiji kawai ke yi abinda yake so

Ubangiji kawai ke yi abinda yake so

- Wannan mutumin ya fadi cewa yaji murnar Ubangiji yayin da yake addu'a

- Yace ance yaje yayi fada da zaki da hannun sa, abunda ya faru ya zama abun tausayi.

Ubangiji kawai ke yi abinda yake so

Yadda da Ubangiji da jin muryar shi babbar baiwa ce, sai dai mutane da yawa sun kasa banbanta muryar Ubangiji ta ainahi da muryar shaidanun aljannu. Zasu ce sunji muryar Ubangiji alhalin kawai zuciyar su ta raya masu ko kuma yaudara ce irin ta shaidanun aljannu.

Wani mutum dan kasar Buenos yace ya samu umurnin da lahira , wai yaji muryar ubangiji inda yace yaje yayi fada da zaki da hannun sa, amma ya manta da wani abu mai mahimmanci cewa duk wani abu na wahayi ko mu'ujiza dole yayi dai dai da karantarwa da littafi mai tsarki, in ka ki wannan gaskiyar to hakika zaka fada cikin yaudara.

Ubangiji kawai ke yi abinda yake so

Ba wata aya a cikin littafi mai tsarki da tace muyi fada da dabbobi masu hadari.

Mutumin ya saurari muryar ba dai dai ba, kuma abun ya koma sai abun ya zamar mai abun kaico, mutumin ya shiga gidan da ake aje dabbobi sai ya haura katanga ya shiga gurin da ake boye zakuna,ya fara fada da zaki, har zakin ta kashe shi.

Wannan ya nuna cewa ba muryar ubangiji yaji ba, saboda ubangiji ba ze taba tura ka inda za'a kashe ka ba, kuma ubangiji ba ze taba cewa kayi fada da wani ba.

Kullum kari ka sauraren abu da kyau karka bi hudubar shaidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel