Barcelona ta maka shugaban La liga kotu

Barcelona ta maka shugaban La liga kotu

- Kungiyar Barcelona ta kai karar shugaban wasannin gasar La liga Javier Tebas a babbar kotun wasanni ta Spain bayan ya soki ‘yan wasan kungiyar kan abinda ya biyo bayan wasansu da Valencia.

- Barcelona dai ta sha da kyar ne a hannun Valencia 3-2.

Barcelona ta maka shugaban La liga kotu
Suarez celebrates a goal with Messi

Magoya bayan Valencia kuma sun jefi Neymar da Messi da Suarez ne da robar ruwa yayin da suke murnar kwallon da Messi ya zira a bugun fanariti a lokacin da ya rage dakikoki a hure wasan.

Shugaban La liga kuma ya ce ‘yan wasan Barcelona ne suka takali magoya bayan Valencia, saboda yadda suka je gabansu suna murna.

Wannan ne dai ya fusata Barcelona har ta kai karar shugaban na La liga.

Hukumar kwallon Spain ta ci tarar Valencia kudi euro 1,500 tare da yin gargadi ga kungiyar akan ana iya daukar matakin rufe filin wasanta idan haka ta sake faruwa.

Ita ma dai Hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA), ta tuhimi kocin Manchester United Jose Mourinho kan ikirarin da ya yi cewa abu ne mai wahala ga alkalin wasa Anthony Taylor ya iya hura wasan da United ta yi da Liverpool.

Mourinho ya kara da cewa nada Taylor domin ya yi alkalancin wasan da suka yi ranar 17 ga watan Oktoba ya matsa masa lamba.

Dokar kwallon kafa dai ta hana koci ya yi tsokaci kan alkalin wasa gabanin a yi wasan.

Yanzu dai an bai wa Mourinho wa'adin ranar 31 ga watan Oktoba domin ya yi bayani kan wannan hali mara kyau da ya nuna, lamarin da ya kaskantar da wasan kwallo.

https://youtu.be/nT0m4FpgP-w

Asali: Legit.ng

Online view pixel