Dan sanda yayi zindir cikin banki a Legas

Dan sanda yayi zindir cikin banki a Legas

- Wani jami’in yan sanda yayi zindir a cikin banki a ranan Litinin 24 ga watan Oktoba

- Yayi hakan ne domin kada a damke shi

- Za’a kama shi da laifin yunkurin cutan wata mata mai mota

Dan sanda yayi zindir cikin banki a Legas

An yi wata taraliya a cikin wata banki a Surulere a jihar Legas a ranan litinin 24 ga watan oktoba inda wani dan sanda yayi zindir haihuwar maihafiyarsa.

Game da cewar Jaridar The Nation, dan sandan yabi wata mata cikin banki ne domin amsan dubuN30,000 a hannunta, yace mata idan suka je ofishin yan sanda N50,000 zata biya.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya zata fara fitar da amfanin gona turai

Amma ba tare da saninsa ba, matan ta kira wata yar fafutuka kuma ta fada mata abinda ya faru. Dan fafutukar ya kira kwamishanan yan sanda, Fatai Owoseni, wanda ya tura jami’ann yan sanda suje bankin da wuri.

Kawai da ya ga jami’an yan sandan, sai ya gudu ya boye karkashin wata mota a wajen bankin amma aka fito da shi

Wani idon shaida yace wanda da aka jawo shi daga karkashin motar ,sai ya fara farka rigar yan sandan sa ,yayi zindir saboda kada a kamashi, amma wasu matasa suka taimakawa yan sandan wajen shigar da shi cikin motan yan sanda.

A bangare guda, jami’an yan sanda jihar Legas sun damke wani mutum, Hyacinth Nwogu, wanda ya damfari wata mata kuma yana fitar da jabun kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel