JTF sun gano kwanyar kwarangwal 25 a Neja Delta

JTF sun gano kwanyar kwarangwal 25 a Neja Delta

- Jami’an gammaya da ke aiki a yankin Neja Delta sun bayyana yadda suka kama wasu mambobin IPOB

- Kana sun bayyana wasu abubuwan ban tsoro da suka gani a dakunan bauta a wasu kananan hukumomi a jihar

JTF sun gano kwanyar kwarangwal 25 a Neja Delta

Jami’an gammaya da ke aiki a yankin Neja Delta karkashin Operation Delta safe, sun bayyana cewa sun samun kwanyar kwarangwal 25 a dakunan bautan wasu yan bindiga a jihar Ribas.

Kana jami’an tsaron sunce sun damke mambonin kungiyar yan asalin Biafra IPOB a jihar Bayelsa.

KU KARANTA: EFCC: An saki Reuben Abati

Yayinda suke bayanin kamun, shugaban yada labarai , Lt-Col Olaolu Daudu,ya baa rahoton cewa rundunar sojin sector 4 a cross riba sun kai hari Ikot Ene Idem, Abakpa da Ikang Inam a karamar hukumar Bakassi da Akpabuyo na jihar.

An gano kwanyar kwarangwal 25 , cikakken kwarangwal da kuma wasu sassan jikin mutane. Bayan sunyi biji-biji da dakunan butan, yace “bayan munyi kaca-kaca da dakunan asirin, mun fitar da yan bindigan Bakassi a inda suke buya. A sani cewa yin amfani da mutane waje yin asiri laifine kuma bazamu yarda da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel