Gwamnatin tarayya zata fara fitar da amfanin gona turai

Gwamnatin tarayya zata fara fitar da amfanin gona turai

- Manoma a Najeriya sun fara girban amfanin gona

- Gwamnatin tarayya zata fara fitar da amfanin gona kasashen waje

Gwamnatin tarayya zata fara fitar da amfanin gona turai
manoma

Hukumar Kastam tace zata fara fitar da amfanin gona kasashen turai daga jihohin Arewa, NAN ta ruwaito.

Kontrollan  jihar Kano da Jigawa, Abutu Mathias,ne ya bayyana hakan a rana Alhamis,27 ga watan oktoba,wajen taron masu ruwa da tsaki a Jihar Kano.

KU KARANTA: Barawon akuya ya dandana kudarsa a Jos

Abutu Mathias,yace wannan shirin zai kaddama ne a watan Nuwamba da Disamba 2016.

Game da cewar sa, hukumar Kastam na shirin taimakawa gwamnatin tarayya wajen tattalin arzikin na rashin dogaro da man fetur.

Yayi kira ga dukkan hukumomi da su bayar da hadin kai da kuma goyon baya domin cimma kudirin mu.

Daya daga cikin nasarorin da hukamar ta samu a wannan shekaran shine harajin da karba a kowani wata a wannan shekara yafi wanda ake karba a shekarun baya 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel