Kyau a fara bincike tun daga mulkin Janar Ibrahim Babangida

Kyau a fara bincike tun daga mulkin Janar Ibrahim Babangida

Daya daga cikin mashawartan Shugaba Buhari ya nemi a fara bincike tun mulkin Shugaba Ibrahim Babangida

- Farfesa Odekunle ya nemi ayi bincike tun daga mulkin Ibrahim Babangida zuwa na Goodluck Jonathan

- Janar Ibrahim Babangida yayi mulkin Soji daga shekarar 1985 zuwa 1993

Kyau a fara bincike tun daga mulkin Janar Ibrahim Babangida

 

 

 

Wani daga cikin ‘yan kwamitin bada shawara game da harkar rashawa ga Shugaban Kasa PACAC ya nemi Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya fara bincike tun daga zamani Janar Ibrahim Babangida. Wannan mutumi ya kuma yaba da kama wasu manyan Alkalan Kasar da aka yi.

Femi Odekunle, wanda Farfesa ne na binciken laifuffuka ya kuma yi kira da Gwamnatin Kasar da ta karbe lambar ban girma da aka ba mutanen da aka samu da laifin cin hanci da rashawa. Tun daga shekarar 1964 aka saba bada lambar ban girma ga wadanda suka yi fice a Kasar.

KU KARANTA: Za a gurfanar da Alkalai a gaban Alkalai

Farfesa Femi Odekunle ya koka da irin barnar da aka yi a Najeriya, yace kamata yayi a fara bincike tun daga zamanin Janar Ibrahim Babangida na Soji wanda ya mulki Kasar na shekaru takwas daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1993. Janar Ibrahim Babangida ya mulki Kasar ne bayan sun kifar da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Soji.

Femi Odekunle, wanda Farfesa ne na binciken laifuffuka yana cikin Kwamitin da Shugaba Buhari ya nada domin ba sa shawara kan yadda za ayi maganin rashawa a Najeriyaya. Farfesa Odekunle yayi wannan bayani ne a Gidan Rediyo na Najeriya watau FRCN a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel