Diraktan Kamfen Jonathan,Muazu ya sheke APC

Diraktan Kamfen Jonathan,Muazu ya sheke APC

- Alhaji Abibakar Habu Mu’azu ya kasance diraktan kamfen Goodluck Jonathan

- Ya sheke jam’iyyar APC kuma ya bayyana dalilinsa na yin hakan

- Jam’iyyar APC a jihar tayi maraba da shi da kuma sauran sabbin mambobin

Diraktan Kamfen Jonathan,Muazu ya sheke APC

Alhaji Abibakar Habu Mu’azu,wanda ya kasance dirktan yakin neman zaben Goddluck Jonathan ya sheke jam’iyya mai ci ta APC.

Mua’zu wanda dan jam’iyyar PDP ne a da  ya dauki katin zama dan jam’iyyar APC a karamar hukumar Akko da ke jihar Gwamba.

KU KARANTA: Ya zama dole a kori Amaechi da sauransu- Afenifere ga Buhari

“Akwai wasu manya wanda suka sheke irinsu tsohon ministan sufuri, Sanata Abdullahi Idris, Tsohon mataimakin gwamnan jihar Lazarus Yoriyo da kuma tsohon ministan FCT, Moddibo Umar.

“Kana Sanata Saidu Rufai Alkali , Jamilu Isisaku Gomna da sauran su wadanda za’a bayyana ida lokaci yayi

 “Tunda mun samu damar yin canji a sama, muna bukatan canji a kasa haka, muna son ya kasance a 2019, Gwambe zata kasance karkashin jam’iyyar APC saboda bamu shiga jam’iyyar domin yankan tketi ba,amma domin mu hada kai domin gyara kura-kuren da akayi a baya da kuma shiryawa gaba.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel