Danniyar Hausa almarace - Reno Omokri

Danniyar Hausa almarace - Reno Omokri

Daga Edita: Akwai zargin cewa Hausawa sun mamaye kuma su ke mulkin kasar yanzu. A wannan kasidar, Reno Omokri na mai ra'ayin cewa arewacin kasar bangare ne mai fadi cike da kabilu amma mutane na yin kuskuren daukar su a Hausawa.

Raba kawuna domin ayi mulki: Idan mu da muke kudancin kasar munce Hausawan arewacin kasar makiyan mu ne, ya kamata mu ankara cewa muna yin rawar 'yan kalilan masu mulki ne wadanda ke mulki ta bayan fage shekara da shekaru wadanda ke son arewacin kasar da kudancin kasar su cigaba da zargin junansu yadda su kuma sai suyi amfani da bangare daya domin cutar da dayan yadda sai su cigaba da mamaye mu.

Idan kai dan kudu ne, ka tambayi kanka, shin su wanene Hausawan da ake cewa na mamaye mu?

A cikin mutane sha ukku da suka mulki kasar nan a matsayin prayim minista ko shugaban kasa tun samun mulkin kai daga turawan Britaniya a 1960, babu daya daga cikinsu wanda yake daga kabilar Hausa.

KU KARANTA: Sojin da suka bace bayan harin Boko haram sun dawo

Tafawa Balewa, prayim ministan mu na farko ya fito daga wata karamar kabila da ake kira Gere a cikin jihar Bauchi. Ana kiran dan kabilar Bagere. Johnson Aguiyi Ironsi dan kabilar Igbo ne daga jihar Abia.Yakubu Gowon Angas ne daga jihar Plateau. Murtala Muhammad, Fulani ne daga jihar Kano yayin da shugaba Olusegun Obasanjo Yoruba ne daga jihar Ogun. Shugaba Shehu Shagari Fulani ne daga jihar Sokoto. Shugaba Muhammadu Buhari, Fulani ne daga jihar Katsina. Shugaba Ibrahim Babangida Gwari ne daga jihar Niger, Ernest Shonekan Yoruba ne daga jihar Ogun yayin da Sani Abacha Kanuri ne daga jihar Borno Duk da yake ya dauki Kano a matsayin jiharsa domin a nan ya girma.

Abdulsalami Abubakar ne kadai shugaba Bahaushe da muka taba yi. Amma shin yayi kama karya?, yayi mamaye?, tabbas a'a. Yayin mulkinsa ya nuna tsoron Allah, ya kuma dauki bangarorin kasar dai- dai. Ya kawo mana jamhuriya ta hudu wadda itace mafi dadewa. Absulsalami mutunen kirki ne.

Bayansa, Obasanjk ya dawo karo na biyu. 'Yaradua ya gaje shi. 'Yar'adua Fulani ne daga jihar Katsina, yayin da wanda ya gaje shi Goodluck Jonathan dan kabilar Ogbia ne daga jihar Bayelsa. Shugaba Buhari da ya gaji Jonathan, Fulani ne.

Fulani sun mamaye Najeriya?: Daga abin da muka Karanta, wasu zasu so yin gyara daga danniyad Hausawa zuwa danniyar Fulani. Wan nan ma zai zama wata almara

Asali: Legit.ng

Online view pixel