Da an kama Amaechi ace ni...- mataimakin shugaban APC

Da an kama Amaechi ace ni...- mataimakin shugaban APC

- Mataimakin shugaban (kudu) na jam’iyyar APC, Segun Oni, yace lokaci zargin da alkalai keyi a kan Amaechi ya kure

- Yace inda ya kasance alkalain babban kotu, da an kama Amaechi

- Oni yace duk wanda yace jam’iyyar APC bazata ta kai labari ba a shekara ta 2019 karda a dauki maganar wannan da muhimmanci

Mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kudu, Segun Oni, yace idan da ya kasance alkalin babban kotu kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi, yayi yunkurin cin nasarar hukuncin kotu ta hanyar cin hanci, da an kama shi.

Da yake Magana ga manema labarai a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba, Oni yace baya a matsayi na kare Ameachi, jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 5 da ya kamata a sani game da angon Fatima Buhari

Da an kama Amaechi ace ni...- mataimakin shugaban APC

Segun Oni, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kudu

Alkalan babban kotu guda biyu wadanda suke karkashin bincike, Sylvester Ngwuta da John Okoro, sun bayyana Amaechi a cikin wani zargi na aikata cin hanci da rashawa.

Mataimakin shugaban na jam’iyyar APC yace baza’a dauki zargin da alkalan keyi a kan ministan sufuri da muhimmanci ba saboda ya zo a kurarren lokaci.

A cewar sa, kamar zuwa ne kace ka ga wani yana aikata fyade a shekarar bara kuma ba kayi komai a kai ba.

Da yake maida martani ga mataimakin sakataren labarai na jam’iyyar ta APC. Timi Frank, wanda yace jam’iyyar na iya tarwasewa a shekara ta 2019, Oni yace ba abune da mai tunani zai furta ba.

KU KARANTA KUMA: Maye yayi hadari a kogin Sapele a hanyarsa ta zuwa Amurka

A ranar Talata, 25 ga watan Oktoba, Frank a yayinda yake yaba ma ci gaban da aka samu kwanan nan a jam’iyyar APC, ya bayyana cewa abubuwa da dama suna afkuwa a cikin kasar nan a yanzu wanda zai iya shafe jam’iyyar APC gaba daya a shekara ta 2019.

Yace hanya daya da za’a iya bi don ceto jam’iyyar shine shugaban kasa ya sanya baki kuma ya goyi bayan ajiye aikin shugaban jam’iyyar ta kasa baki daya, Cif John Odigie-Oyegun.

Shugabannin jam’iyyar ta APC shun yanke hukuncin bincikar Frank kan zargin haddasa ayyukan jam’iyya kuma zasu dakatar dashi idan aka kama shi da laifi.

https://youtu.be/_Sfn8flQlVU

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel