Babban Limami Sheikh Kilbani zai zo Najeriya

Babban Limami Sheikh Kilbani zai zo Najeriya

- Babban Limami na Masallacin Harami na Makkah zai zo Najeriya a karshen shekarar nan

- Sheikh Adil Kilbani zai yi magana ne tare da sauran Malaman addini

- Sauran manyan Malamun addini za su halarci wannan taro

Babban Limami Sheikh Kilbani zai zo Najeriya
Sarkin musulmai Alhaji Muhammad Sa'ad

 

 

 

 

 

 

Babban Limami Sheikh Adil Kilbani na Masallacin Harami da ke Gari mai tsarki na Makkah zai kawo ziyara Najeriya inji Jaridar Daily Trust. Wannan Babban Limami zai zo wani taro ne da Kungiyar Musulmai ta Ummah ta shirya na kwana uku a Garin Abuja.

Sauran Malaman addinin Kirista za suyi jawabi a wurin wannan taro, irin su Fasto Tunde Bakare na Legas, da kuma Bishof Mathew Hassan Kukah da ke Sokoto. Za a gudanar da wannan taro ne a tsakanin 2 zuwa 4 ga watan Disamba mai zuwa.

KU KARANTA: A koma tsarin tattalin arzikin musulunci

Sauran Manyan Malamai da Shugabannin addini za su halarci wannan taro, kamar su Mai Girma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad III, Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II da kuma Shehun Borno Alhaji Umar Ibn Abubakar. Manyan Malamai irin su Sheikh Aasim Al Hakim daga Saudiyya da kuma Yvonne Ridley daga Kasar Birtaniya, sannan Kuma Sheikh Dr. Isa Ali Fantami; Darektan NITDA na Najeriya za suyi magana a wajen taron.

Amir din Kungiyar Ummah na Musulunci Malam Abubakar Sadiq Muhammad yace za ayi wannan taro ne domin karawa juna fahimtar musulunci da kuma agazawa ‘Yan gudun Hijira da rikicin Boko Haram ta rutsa da su a Arewa maso gabashin Kasar nan.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel