Chelsea taji mamaki da fidda ita da West Ham

Chelsea taji mamaki da fidda ita da West Ham

West Ham ta fidda kungiyar Chelsea da kuma Antonio Conte yayi magana akan wasan.

Manajan kungiyar Chelsea wato Antonio Conte, ya bayyana yadda kungiyarsa tayi rashin nasara dangane da fidda ita da akayi a gasar cin kofin EFL.

Kungiyar West Ham dai sunyi nasaran doke kungiyar Chelsea ne daci 2-1 a filin wasa na Olympic wanda hakan ya baiwa kungiyar ta West Ham din dama tsallakawa a wasan zagaye na kwata fainal.

Kwallayen da Cheikhou Kouyate dana Edimilson Fernandes da suka samu daman zurawa a ragar na Chelsea wanda daga baya kuma dan wasan Chelsea wato Gary Cahill ya samu nasarar zura kwallo daya cikin minto 90 inda wasan ya kare daci 2-1. Inda yan Chelsea suka barar da wasu damar maki da suka samu wanda suka hada da shan karfen mai tsaron gidan abokan hamaiyar nasu.

Bayan an gama wasan ne Conte yace, munsan irin wannan wasan yana da wuyan gaske, haka kuma mun samu damar maki sosai wanda ya kamata ace muci, amman kuma bamu samu sa'ar hakan ba, dukda dai nasan munyi kokari sosai munyi wasa mai kyau, naga hazaka sosai a wajen yan wasana musamman alokacin da aka kusa tashi wasan, inda mukayi kokarin muga mun rama kwallayen da aka zura mana, amman bamu samu sa'a ba.

Dan kasar Italiyan yaci gaba da cewar, " bamuyi tsammanin wannan kwallon ta biyu ba da wuri haka, wanda hakan ya canza mana tsarin mu da wuri ya janyo mukayi canjin da bamuyi niyyaba, amman kuma duk da haka bamu samu sa'ar ramawa ba sai gab da za'a tashi muka samu damar zuwar kwallo daya. Aboda haka munyi rashin nasara a wannan lokacin.

Chelsea taji mamaki da fidda ita da West Ham
Antonio Conte

Ya kara dacewa, wannan kofin yanada matukar mahimmanci ta wajen kwada yara masu tasowa a kungiya. Munada yara masu kyau kuma wa'anda suke sha'awar buga wasa mai kyau domin kuwa na gamsu da yadda yaran ke buga wasan su ta yarda suke nuna cewar suna da hikima tare da nuna bajinta a wasannin da suka buga. Inada matukar tabbaci akan abun da yara suke bugawa cewar zasu zama wani abu nan gaba.

Kocin dai ya karkare maganan sane da cewar, koda yake kafi gane matsalar ka idan aka cika bawai sai kaci wasaba. Saboda haka ina da tabbaci akan yarana, suna da matukar mahimmanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel