Maye yayi hadari a kogin Sapele a hanyarsa ta zuwa Amurka

Maye yayi hadari a kogin Sapele a hanyarsa ta zuwa Amurka

- An gano wani da yayi ikirarin shi maye ne a cikin wani kogi dake Sapele

- Mutumin yayi  ikirarin cewa ya tashi zuwa Amurka ne lokacin da man sa ya kare

- Ya daura laifin matsalar da ya samu a kan koma bayan tattalin arziki da ake ciki

Wani mutumi da yayi ikirarin shi maye ne ya ga laifin koma bayan tattalin arziki na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dalilin da ya sanya sa yin hadari a kogin Sapele.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mutumin da aka gano a cikin kogin Ajogodo a Sapele, jihar Delta ya bayyana cewa ya tashi ne daga filin jirgin sama na Benin don halartan wani taro a kasar Amurka, ya kuma yi amfani da ganyen ayaba ne gurin tashi.

KU KARANTA KUMA: Ana zargin sarauniyar kyau ta jihar Anambra da aikata madigo

Ya ce ya kamata ya kalli wani wasan kwallon kafa ne a kasar Amurka lokacin da man jirginsa ya kare.

Ya ce: “Na tashi sama ne da abunda a bayyane ake kira da ‘bawon ayaba’, amma a zahirin gaskiya ya kasance jirgin sama na mai tsada.

Maye yayi hadari a kogin Sapele a hanyarsa ta zuwa Amurka
Maye yayi ikirarin yana hanyarsa ta zuwa Amurka lokacin da man sa ya kare

“Ya yi hadari dani zuwa wannan gada, lokacin da man ya kare.  Yan kungiyana zasu zo da daddare don su cika mun da mai, saboda na samu na ci gaba da tafiyata zuwa kasar Amurka.

“Ya zama lallai na kasance a kasar Amurka don kallon wasan kwallon kafa, saboda akwai koma bayan tattalin arziki, da kuma rashin aikin yi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel