Hauka! Ya makale a cikin kwandon shara

Hauka! Ya makale a cikin kwandon shara

Wani abin dariya kuma abin al'ajabi ne ya faru yayain da wani mutum ya zama abin kallo bayan ya makale a cikin kwandon shara kuma ya gagara fita a garin Murcia dake kudancin kasar Sifen.

Hauka! Ya makale a cikin kwandon shara

Rahotanni sun bayyana cewa yayin da jama’a suka fara jin murya na fitowa daga kwandon sharer ne suka sanar da yansanda. Zuwan yansanda keda wuya su ciro shi, inda daga nan ne ya musu bayanin cewa yaje roran tsofaffin kaya ne a ciki sai ya makale.

Sai dai mutumin ya kwashe fiye da awanni hudu a cikin kwandon sharar ba tare da mutane sun kai mai agaji ba, saboda a tunaninsu wasan kwaikwayo a keyi. Sa’ar shi daya da jami’an yansanda suka iso wurin.

KU KARANTA: Tsohon dan wasan Arsenal, Henry ya yaba ma Pogba

Hauka! Ya makale a cikin kwandon shara

Sai dai abin mamaki anan shine ta yaya mutum zai kai kanshi cikin kwandon shara, duk da haka wannan wa’azi ne ga mutanen da basa lura da kyau da idon basira kafin su afka ma wani aiki.

Idan kai ne ya zaka yi idan kaji murya da motsin mutum a cikin kwandon shara?

Asali: Legit.ng

Online view pixel