Babu maganar kara kudin man fetur-Inji NNPC

Babu maganar kara kudin man fetur-Inji NNPC

Mai magana da bakin Kamfanin NNPC na Kasa yace babu shirin kara kudin man fetur a Kasar

NNPC tace akwai doguwar yarjejeniya tsakanin Kamfanin Kasar da masu shigo da man fetur din

Garba Deen yace akwai isasshen man fetur a Kasar

Babu maganar kara kudin man fetur-Inji NNPC
NNPC

 

 

 

 

Mai magana a madadin Kamfanin man Kasar nan watau NNPC, Garba Deen Muhammad yace babu wani shirin kara farashin man fetur a Kasar. NNPC tace tana da tsarin da zai cigaba da samar da man fetur ga Kasar har na wani dogon lokaci, wanda hakan ba zai bada damar a taba kudin ba.

Garba Deen din yayi karin haske ne a game da kalaman da wani babban Jami’in Kamfanin man Kasar yayi, inda yake cewa ba zai yiwu ace ba a kara kudin man fetur din ba. Garba Deen yace ba a fahimci abin da wannan jami’I yake nufi bane, yace amma a hakikanin magana, babu maganar karin kudin man fetur.

KU KARANTA: Kamfanin Dangote ya kori Ma'aikata

Mai magana da yawun bakin NNPC yace idan har ta kama za a kara kudin man fetur din, to Hukumar PPPRA-mai kula da farashin kayan mai za tayi wa mutanen Kasa jawabi da dalilin da ya sa za a dauki wannan mataki, yace amma a yanzu, babu ma wannan batu.

NNPC tace tana da doguwar yarjejeniya tsakanin Kamfanin Kasar da masu shigo da man fetur din na wani lokaci, sannan kuma an shawo kan duk matsalolin da ake samu a baya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel