RA'AYI: Ina mai kare Amaechi, da'a da sanin ya kamata

RA'AYI: Ina mai kare Amaechi, da'a da sanin ya kamata

Daga Edita: Labarai sun fito na zargin cin hanci da ake ma wani tsohon gwamna kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi daga wasu alkalai buyu na kotun koli, zargin da ministan ya karyata.

Wani marubuci kuma mai sharhi kan harkokin zamantakewa Nkechi Odoma na mai ra'ayin cewa zargin cin dunu ne alkalan ke yima Amaechi.

'Yan Najeriya na amfani da cin dunu a matsayin makami domin nuna rashin laifinsu duk lokacin da suka ga an kusa kama su da wani laifi. Lokutta da yawa yadda 'yan Najeriya ke amfani da cin dunu nada rudaswa da murde da'a kuma da karya dokar kasa.

Duk da yake ana binciken alkalai da dama, amma batun alkalai biyu na kotun koli John Iyang Okoro da Sylvester Ngwuta wadanda DSS ta kaima hari, ta kama su kuma ta tsare kan zargin cin hanci irin na alkalai ya dauki wani salo maras kan gado. Sun hada kai suka fito suka gaya ma jama'a yadda tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan sufuri Rotimi Chubuike Amaecchi yayi kokarin basu cin hanci.

Sun zargi Amaechi da hannu cikin muzguna masu da ake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel