Abati na bayyana mana yadda sukayi bannar kudi - EFCC

Abati na bayyana mana yadda sukayi bannar kudi - EFCC

- Hukumar EFCC t bayyana cewa bata damke Reuben Abati ba

- Ta ce innama gayyatarshi tayi kuma ya amsa gayyatar

Abati na bayyana mana yadda sukayi bannar kudi - EFCC

Hukumar hana Almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa,EFCC ta bayyana dalilinta na tsare Reuben Abati, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

A wata jawabin da tayi a gurguje a shafin ta na Facebook a yau talata,25 ga watan oktoba, hukumar yak da rashawan tace Abati ya kasance a ofishinsu ne bisa ga gayyatar da sukayi masa domin bayani akan bannar kudin ka akayi a ofishinsa na da.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta sauya ra’ayi, zata sasanta da tsagerun Neja Delta

Jawabin tace: “Tsohon mai Magana da yawun shugaban kasa, Dr. Reuben Abati ,ya amsa goron gayyatar da hukumar EFCC sukayi masa zuwa ofishin ta da ke Abuja."

A yanzu haka, yana bayyana ma jami’an EFCC rawan ya taka wajen bannar kudin kasa ta ofishin sa. Zamu fada muku abin ya wakana.

Wannan na zuwa ne bayan rahoton cewa hukumar EFCC ta damke tsohon ministan birnin tarayya Abuja, Bala Mohammad a ranan Litinin. Kuma yana bayar da jawabai masu amfani

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel