‘Yan Sanda sun kama wata mata

‘Yan Sanda sun kama wata mata

- Jami’an ‘yan Sanda sun kama wata Tsohuwa ta saye jinjiri dan wata biyu da haihuwa

- Yanzu haka Miss Ross Edward na nan a tsare wajen Hukuma

- Uwar wannan Jinjiri ta sayar da shi N450, 000 saboda talauci

Jami’an ‘Yan Sanda sun kama wata mata mai suna Miss Ross Edward dauke da jinjiri dan wata biyu. Wannan mata ta bayyanawa Jami’an ‘Yan Sanda cewa ta saye wannan jinjiri ne daga hannun mahaifiyar sa kan kudi N450, 000

Cordelia Mani Nwanwe, Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Akwa-Ibom, ya tabbatar da faruwar wannan abu, ya kara da cewa akwai wani likita mai suna Dakta Eneyo Nyang da aka hada kai da shi wajen sayar da wannan jinjiri. Jami’in ‘Yan Sandan na Jihar yace za su cigaba dayin iyaka kokarin su wajen aikin kare rayuwkar jama’a a Jihar.

KU KARANTA: An same ta da kwaya a rigar mama

Mahaifiyar wannan jinjiri tace babu ce ta sa ta sayar da diyar da ta haifa, uwar jinjirin Miss Comfort Effiong tace ba ta da kowa; uwar ta tana fama da rashin lafiya, sannan kuma mijinta ya rasu. Wannan mata tace ta rasa yadda za tayi a duniya, hakan ta sa ta sayar da jinjiri dan wata biyu domin samun kudi.

Wannan mata watau Miss Ross Edward tace tana da sha’war da, shiyasa ta saye wani jinjiri. Mahaifiyar jinjiri tace dai ba ta da wanda zai kula da yaron ko ya zauna hannun ta, shiyasa ta sayar N450000.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel