Osaze ya koma buga wasa a kasar Ingila

Osaze ya koma buga wasa a kasar Ingila

Fitaccen dan wasan Najeriya Osaze Odemwingie ya koma harkar buga tamola a kungiyar Rotherham dake rukuni na biyu a kasar Ingila.

Osaze ya koma buga wasa a kasar Ingila

A baya dai Osaze ya buga ma kungiyoyi daban daban ciki har da Cardiff, Stoke City da West Bromwich Albio duk a gasar Firimiya ta Ingila. Bugu da kari Osaze yayi wasa a kugiyar Lille ta kasar Faransa da Lokomotiv Moscow ta kasar Rasha.

Cikin wata sanarwa da kungiyar Rotherham ta fitar a shafinta na yanar gizo, tace “Rotherham United ta kammala cinikin dan wasan gaba Peter Odemwingie akan yarjejeniya ta gajeren zango zuwa watan Janairu.”

KU KARANTA: An tsinci gawar direban Yar'Kurkura a kango

Sanarwar ta cigaba da fadin: “Odemwingie ya zamto siyayyan farko da sabon mai horar da kungiyar Kenny Jackett yayi, bayan ya rattafa hannu akan yarjejeniyar da yammacin jiya Litinin a filin wasa na AESSEAL. Kwarerwar dan wasan abin koyi ne bayan ya buga a rukunin manyan kugiyoyi a gasar Firimiya, ciki har da West Brom da Stoke City.

“Sa’annan harkar doka tamola ta kais hi har kasar Faransa inda ya buga ma kungiyar Lille da Lokomotiv Moscow. Osaze mai shekaru 35 ya buga ma Bristol City bayan ya ya bar Stoke City a kakar bara.”

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel