Muhimman labaran ranan litinin

Muhimman labaran ranan litinin

Jardiar Legit.ng ta tattaro muku muhimman labaran ranan litinim 25 ga watan Oktoba, 2016.

1. Ganduje na shirin bincikar gwamnatin Kwankwaso

Muhimman labaran ranan litinin

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi barazanar bincikar gwamnatin wanda ya gada Rabi'u Kwankwaso.

2. Manyan lauyoyi sun samu sabani akan dakatad da Alkalai

Muhimman labaran ranan litinin

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa wasu manyan lauyoyi da masu ruwa da tsaki sun samu sabani akan zancen dakatad da lauyoyin hukumar DSS ta kai wa farmaki har gida. Duk da cewan Majalisar shari’ar tarayya ta ki Maganar dakatad dasu amma manyan lauyoyi sun ce a dalkatad da su.

3. Saurayi ya nemi a aurar masa da daya daga cikin ‘yan matan Chibok

Muhimman labaran ranan litinin
Mohammed Adamu Danladi

Wani matashi mai suna, Mohammed Adamu Danladi, ya aika wata sako ga shugaba Muhammadu Buhari akan yan matan chibok 21 da aka saki.

4. Cin hancin N500m na MTN: Abba Kyari na rokon DSS, 'yan sanda su bincike shi

Muhimman labaran ranan litinin
Abba Kyari

Abba Kyari, shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa ya rubuta ma daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da babban speton 'yan sanda da su binciki zargin da ake masa na amsar N500m na toshiyar baki daga MTN.

5. Dalilin daya sa na sace karamar yarinya, na kuma yi mata fyade - Direban keke

Muhimman labaran ranan litinin

Wani direban keke (keke NAPEP) dan shekara 28 Dada Azeez ya fada hannun 'yan sandan gaggawa da ake kira Rapid Response Squad (RSS) na jihar Lagos domin satar wata Karamar yarinya, Punch ta ruwaito.

6. Wajibi ne Buhari ya sa a binciki Amaechi- PDP

Muhimman labaran ranan litinin

Jam’iyyar PDP shiyar jihar Ekiti tayi kira ga shugaba Buhari ya bada umurnin bincikan daya daga cikin ministocinsa ,Rotimi Amaechi bisa ga tuhumar da Jastis Sylvester Agwata da Nyang Okoro sukayi masa.

7. Buhari da APC nayi ma Amaechi labile - IPOB

Muhimman labaran ranan litinin

Kungiyar masu yaki neman biyafara wato Indigenous People of Biafra (IPOB) sun siffanta jam’iyyar APC a matsayin gun gun macuta

8.Ikon Allah: Jaririn da aka Haifa sau biyu

Muhimman labaran ranan litinin

Wata mata a birnin Texas ,kasar Amurka , Margaret Boemer,ta shiga wani halin da sai da aka ciro dan da ke mahaifan ta kusan makonni 12 da haihuwa saboda wata cuta da ke cikinta.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel