Dalilin musifa a Nigeria

Dalilin musifa a Nigeria

- Wani babban mai wa’azin addinin kirista ya ce kisan gillan da a ka yiwa su Tafawa Balewa ne har yanzu ke bibiyan Najeria kuma shi ne ya jefa Najeriya cikin matsala

- Babban mai wa’azin ya yi kira ga 'yan Najeriya da su dage da addu'a dan kawar da wannan annoba kisan wadanda ba su ji ba, ba kuma su gani ba

Dalilin musifa a Nigeria
Tafawa Balewa

Wani  mai wa’azin addinin Kirista Babatunde Ayodele ya ce, Najeriya ba za ta taba zama lafiya ba saboda mummunan kisan gilla da a ka yi wa Firayi Ministan farko na Najeriya Abubakar Tafawa Balewa wanda aka kashe shi a juyin mulki na farko a watan Janairu 1966.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, malamin addinin ya ce, Najeriya tana fuskantar matsaloli ne saboda annobar kashe mutumin da bai ji ba bai gani ba, ya na kuma yi gargadin cewa, in har ba a dage da addu'a  ba, annobar za ta ci gaba da zama sakamakon kisan gillan na shekaru 50.

KU KARANTA KUMA: Ikon Allah: Jaririyar da aka Haifa sau biyu

Kashe-kashe da kalubalen da gwamnatin Buhari ta ke fuskanta abin takaici ne, amma alhakin jinin Firayi ministan Najeriya na farko kuma tilo, da a ka zubar bisa zalunci, shi ne ya ke bin Najeriya har yanzu. Sannan ya kuma ce,

" Kisan gillar ya Kawo masifa a Najeriya shi ya sa duk yanda gwamnati mai ci ta ke kokarin kamanta adalci mutane sai korafi su ke yi. Abinda Najeriya ke bukata yanzu shi ne addu'a matuka, dukkan bangarorin addinai sai sun hada kai sun yi addu'a yanda kowane addini ya koyar, domin a kawar da wannan masifar ta Kisan Tafawa Balewa da bai ji ba bai gani ba."

Har ila yau ya yi kakkausar suka ga sauran malaman kiristanci kan gum da su ka yi da bakinsu suna gani a na muzgunawa kiristoci a kasar nan. Ya zayyana sunayen fasto Enoch Adeboye na Redeemed Christian Church of God, da Bishop David Oyedepo na Living Faith Church, da kuma William Kumuyi na Deeper Life Ministry, da cewa sun yi shiru yayin da kiristoci ke cikin matsanancin hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel