Jariri ya tsira daga hadarin jirgin kasa a Kamaru

Jariri ya tsira daga hadarin jirgin kasa a Kamaru

Zakaran da Allah ya nufa da cara, ana mazuru ana shaho sai yayi, inji Bahaushe.

Jariri ya tsira daga hadarin jirgin kasa a Kamaru

A nan ma wani jariri ne da Allah ya kaddara yana da sauran kwana a gaba ya tsira daga wani mummunar hadari data lakume mutane sama da 73.

Mumman hadarin ya auku ne a ranar Asabar 22 ga watan Oktoba a garin Eseka dake birnin Yaounde na kasar Kamaru, inda aka samu mace mace sama da 73 tare da jikkata mutane sama da 600. Tuni dai gwamnatin ta bayyana ranar zaman makoki.

Jariri ya tsira daga hadarin jirgin kasa a Kamaru
Jariri ya tsira daga hadarin jirgin kasa a Kamaru

Rahotannin sun bayyana cewa hadarin ya faru ne sakamakon cika jirgin da aka yi da mutane fiye da yadda yake dauka, kuma sai jirgin ya kauce hanyar sa saboda nauyi da yayi mai yawa a garin Eseka. Sai dai ana cikin tantance gawawwakin ne aka tsinci wani jariri da ransa, sai dai bicike ya nuna iyayensa duka biyu sun rasa rayukansu a cikin hadarin.

KU KARANTA: Barawao ya yaba ma aya zaki a hannun jama’a

Wani ma’abocin shafin Facebook Mouise Tanyi ya watsa bidiyon yadda abin ya faru, tare da sunayen wasu daga cikin mamatan. Sa’annan ya kara da cewa gwamnatin kasar zata bayyana ranakun zaman makokin wadanda suka rasu.

Jariri ya tsira daga hadarin jirgin kasa a Kamaru

“wannan shine jerin sunayen wadanda suka rasu a hadarin jirgin kasa daya faru a Kamaru. Shugaban kasa Paul Piya ya bayyana ranar Litinin 10/24/2016 a matsayin ranar zaman makoki.

Muna fatan gwamnati zata dauki nauyin wannan jariri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel