Mourinho da tsohon dan wasa sun soki Paul Pogba

Mourinho da tsohon dan wasa sun soki Paul Pogba

Shahararren tsohon dan wasan Manchester United Gary Neville ya bi sahun masu sukan dan wasan daya fi kowa tsada a duniyar kwallo Paul Pogba saboda rashin tabuka abin a-zo-a-gani a wasan kungiyar da Chelsea a ranar Lahadin data gabata.

Mourinho da tsohon dan wasa sun soki Paul Pogba

Shima mai horar da Manchester Mourinho bai ji da dadi ba a hannun tsohuwar kungiyar sa Chelsea inda suka lallasa shi ci 4-0. Wasan yayi zafi yadda ake tsammani, sai dai kungiyar Chelsea ita ta samu nasara.

Gary Neville ya bayyana bacin ransa da tsarin wasan tsaron gida da Manchester tayi amfani da shi, “abin kunya ne ace Kante ya keta tsakanin Herreira da Pogba yaci kwallo, bayan su yan wasan tsakiya ne, kuma Hazard ne ya ba shi kwallon. Kwallon farko da aka ci kuwa abin dariya ne.” inji Neville

KU KARANTA: An caccaki Ronaldo saboda cin mutuncin addinin Buddha

Dan wasan ya cigaba da bayyana bacin ransa yana cewa “Manchester ta kashe pan miliyan 180 a siyan yan wasan tsakiya, amma har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

A baya ma dai kocin Manchester ya soki Pogba inda yace “zatona shi ne idan Pogba na cikin fili, zamu samu daman fasa masu tsaron gidan Chelsea. Amma a fannin tsaron gida mun danyi kokari, sai dai muna bukatan sake zade damtse.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel