Hukumar EFCC ta kwakulo sirrin Patience Jonathan

Hukumar EFCC ta kwakulo sirrin Patience Jonathan

- Hukumar EFCC ta bi diddigin albashin Tsohuwar Uwargidar Najeriya Patience Jonathan

- EFCC tace albashin Patience Jonathan bai isa ace ya gina mata wadannan manyan Otel da ta mallaka ba

Hukumar EFCC tace sai Madam Patience Jonathan tayi bayanin inda ta samu Dala Miliyan $15

Hukumar EFCC ta kwakulo sirrin Patience Jonathan
Patience Jonathan

 

 

 

 

 

 

 

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta tasa Tsohuwar uwargidar Najeriya Dame Patience Jonathan a gaba. Hukumar ta EFCC ta bi diddigi ta gano ainihin albashin da Patience Jonathan ta ke karba a wancan lokaci, ta tabbatar da cewa albashin na ta bai isa ya gina Otel ba.

Jaridar ‘The Nation’ ta rahoto cewa Albashin Matar Tsohon Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan a lokacin da ta ke rike da mukamin Sakataren Din-din-din bai wuce N700,000 ba. Sai dai kafin saukar mijin ta mulki, Patience Jonathan ta gina manyan katafarn otrl guda 2, da kuma manyan gidaje har guda 9, da wani makeken shago guda.

KU KARANTA: Hukumar EFCC tayi ram da wasu mutane

Wani Jami’in Hukumar EFCC yace dole sai Tsohuwar uwargidar Najeriyar Dame Patience Jonathan tayi bayanin inda ta samu irin wannan kudi haka, don a binciken da suke gudanarwa, sun gano albashin ta, kuma ba su isa ace tayi wannan gine-gine ba.

Hukumar EFCC dai sun tasa Madam Faka Patience Jonathan gaba, cewa sai tayi bayanin wadanda suka ba ta kyautar kudin da suke akaun din ta har Dala Miliyan $15. Madam Patience Jonathan din dai tace ‘Yan uwa ne da abokan arziki suka yi ta ba ta gudumuwa a baya.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel