Ban yarda an sace 'yan matan Chibok ba - Fayose

Ban yarda an sace 'yan matan Chibok ba - Fayose

- Gwamna Fayose ya sake jaddada shakkunsa kan satar fiye da 'tan mata 200 daga Chibok

- Yace ana yin abubuwa da yawa a asirce

- Yace yarinya ta farko da aka saki bata ko iya magana da harshen Ingilishi duk da yake dalibar kimiyya ce

Ban yarda an sace 'yan matan Chibok ba - Fayose
Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yan matan Chibok

Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya sake nuna shakka game da satar fiye da 'Yan matan makarantar gwamnati ta mata ta garin Chibok 200 da akayi cikin Aprilu 2014 a jihar Borno. Yace har yanzu bai yarda an sace yaran ba domin ana yin abubuwa a asirce. Gwamnan ya fadi haka a wani shiri da gidan talabishin na Channels mai suna Hard Copy ranar Juma'a 21 ga Oktoba

KU KARANTA: An kama wata mata da kwayar koken a cikin rigar mama

Yace: "Ina cikin duhu game da 'yan matan Chibok. Fiye da dalibai 200 zasu je yin jarrabawa kan kimiyya. Zasu yi jarrabawa kan kimiyya amma ta farko da suka kawo bata iya magana da harshen Ingilishi, yayin da ta biyu gungun 'bring back our girls' suka kangeta. In ka kalli abinda ya faru sai ka fara tambaya shin wannan gaskiya ne kusa?"

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel