Hadiza Buhari-Bello tayi kaca-kaca da ‘Yan Kungiyar BBOG

Hadiza Buhari-Bello tayi kaca-kaca da ‘Yan Kungiyar BBOG

Diyar Shugaban Kasa, Hadiza Buhari-Bello tayi raddi ga ‘Yan Kungiyar BBOG

Hadiza Buhari-Bello tace ba abin da zai sa ta ci kudin wasu mutane

Madam Oby Ezekwensili ta zargi diyar Shugaban Kasar da kokarin yin amfani da sunan su

Hadiza Buhari-Bello tayi kaca-kaca da ‘Yan Kungiyar BBOG
Yar shugaban kasa, Hadiza Buhari Bello

Diyar Shugaban Kasa, Hadiza Buhari-Bello ta maida martani ga Madam Oby Ezekwensili ta Kungiyar BBOG masu fafutukar ganin ‘Yan matan Chibok sun dawo gida. Oby Ezekwenisili ta zargi diyar Shugaban Kasar da yin amfani da sunan su wajen samun alheri.

Jagorar Kungiyar BBOG watau BringBackOurGirls, Madam Oby Eze, ta zargi Kungiyar AFRISEI ta su Hadiza Buhari-Bello da kokarin yin amfani da sunan su wajen neman gudumuwa ga ‘Yan matan Chibok. Oby Ezekwensili tace jama’a su bi a hankali da Kungiyar AFRISEI domin su ‘Yan BBOG ba su san da zaman sa ba.

KU KARANTA: Chimamanda Adichie ta soki Shugaba Buhari

Sai dai diyar Shugaban Kasar Hadiza Buhari-Bello, tace ba ta bukatar amfani da sunan BBOG domin taimakon yaran na Chibok da aka sace. Tace don haka ba ta bukatar komai ko kokarin satar wani abu daga gare su. Hadiza Buhari-Bello tace an san da zaman Kamfanin ta a Kasa, domin tana da Satafiket na bude Kamfani, kuma tana da irin nata manufar mai zaman kan ta.

Hadiza Buhari-Bello, tace aikin wannan Kamfani nata agazawa marasa karfi kamar irin su Matan Chibok da sauran wadanda ‘Yan Boko Haram suka sace. Diyar Shugaban Kasar tace ba ta bukatar kama kafa da Kungiyar BBOG domin taimakon ‘Yan Matan na Chibok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel