Ganduje, Ka cire mana jar hular mu-Kwankwasiyya

Ganduje, Ka cire mana jar hular mu-Kwankwasiyya

– ‘Yan Kwankwasiyya sun kira Gwamna Abdullahi Ganduje da ya tube masu Jar hula ko kuma su kai sa Kotu

Kwankwasiyya sun ce Ganduje ya bar akidar don haka babu dalilin cigaba da zama da alamar su

Rikicin Ganduje da Tsohon mai gidan na sa Kwankwasiyya na ta kara cabewa

Ganduje, Ka cire mana jar hular mu-Kwankwasiyya

A jiya DailyTrust ta rahoto cewa magoya bayan Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ‘Yan kwankwasiyya’ sun nemi Gwamna Dr. Ganduje na Jihar Kanon da ya tube jar hular da ke kan sa, idan ba haka ba kuma za su shiga Kotu da shi nan da kwana biyu.

‘Yan Kwankwasiyya sun ce Gwamna Ganduje ba ya tare da su cikin tafiyar, don haka babu dalilin cigaba da saka jar hular Kwankwasiyya. A jiya ne dai Tsohon Gwamnan Kano kuma Shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso ya cika shekaru 60.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai saki wasu kudi

Haka kuma tafiyar Kwankwasiyya ta cika shekara 6 kenan a duniya, a wajen bikin murnar cika shekarun Tsohon Gwamnan ne, wani mabiyin Kwankwasiyya, kuma Shugaban Hannun karba-Hannun badawa, Alhaji Sharu Gwammaja yace dole fa Gwamna Ganduje ya cire jar hula tun da yanzu ya baude.

Alhaji Sharu Gwammaja yace sun ba Gwamnan awannin 48 da ya cire hular ko su shiga Kotu

‘Yan Kwankwasiyya sun ce Ganduje na cin alfarmar jar hula wajen mutanen Kano, duk cewa ba dan ta bane. ‘Yan Kwankwasiyya sun ba mutanen Kano hakuri da suka tsaida masu Ganduje a matsayin Gwamna, suka ce ai an kuma gama.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel