An kwashe kimanin mutane 500 a filin jirgin sama na Landan

An kwashe kimanin mutane 500 a filin jirgin sama na Landan

BBC sun rawaito cewar, wani sinadari da ake tunani ya janyo dalilin da yasa aka dakatar da aiki a filin sauka da tashi jiragen sama na Landan a ranar Juma'a, 21 ga watan Oktoba.

Jaridar British News Agency, ta rawaito cewar a kalla mutane 500 ne aka kwashe a filin jirgin saman saboda tsoro.

An kwashe kimanin mutane 500 a filin jirgin sama na Landan
Fasinjoji a filin jirgin saman landan

BBC sun bayyana cewar, yan kwana-kwana na gabashi Landan sun fidda mune 500 daga cikin filin jirgin saman da misalin karfe 4, bayan da wasu fasinjoji kamu da rashin lafiya. Haka kuma an bayyana cewar jami'an kiwon lafiya sunyima mutane 26 magani ta amfani da motar asibiti, a inda kuma aka kai mutane guda biyu asibiti.

Lamarin dai ya sanya aka tilastama mutane barin filin jirgin saman, inda kowa ya fita da misalin karfe 7:00.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace Muhammad Madoki

An kwashe kimanin mutane 500 a filin jirgin sama na Landan
Fasinjoji a wajen filin jirgin saman na Landan

Haka kuma, BBC sun bayyana cewar babu wani alamar sinadari da aka samu a binciken da akayi.

Haka kuma, acewar jami'an yan kwana-kwanan ankai sumame harso biyu alokacin da jami'an kwana-kwana da yan sanda sukayi a wasu gine gine dake cikin filin jirgin sama inda suka sanya kayan kariya dan gudun kada su cutu.

Hardai aka gama binciken, ba'a samu komai ba, inda akayi duk binciken daya kamata ayi domin a tabbatar da babu sauran wani abun cutar wa a filin jirgin.

Wani da abun ya faru a gaban sa mai suna Chris Daly dan shakara 35 wanda yake Southen. Inda ya shaidama BBC cewar ya dawo daga tafiya a jirgin BA daga Glasgow a inda yakejin labarin al'amarin daga hukumomin kwana-kwana na filin jirgin saman.

KU KARANTA KUMA: Wata malama tayi lalata da dalibai

Alokacin da suka shigo cikin dakin da matafiyan suke jira sai kawai mukaji ana kada karaurawar alamar babu lafiya, a inda akayi magana da yare kala uku, inda aka cewar akwai matsala a filin jirgin saman, saboda haka ana shawartar matafiyan da suke cikin dakin jira da kuma cikin filin jirgin dasu bar wajen maza-maza sufita wajen harabar filin jirgin saman.

Inda duk muka rasa abinda zamuyi saboda rudewa, duk muka tsaya a inda jirage suke iskan jirgi yana ta hura mu, domin kuwa wani jirgi dake kusa damu ya fara shirin tashi.

Haka kuma ina ganin wasu jirage sunata shawagi a sararin samaniya amman babu jirgin daya sauka kasa, kuma babu wanda yace mana ga abinda yake faruwa, mudai kawai munga ma'aikatan kwana-kwana suna ta bincike a cikin gine ginen dake filin jirgin saman.

Saidai nagani a shafin Tweeter ana cewar wai da yiwuwar wani sinadari ne mai hatsarin gaske ya fashe a wani sashen na filin jirgin saman. Amman nidai ban damu ba, saboda mudai muna waje.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel