MOPPAN tace zata kori Ali Nuhu idan yayi laifi

MOPPAN tace zata kori Ali Nuhu idan yayi laifi

- Bayan kwanaki da korar yar wasan hausar nan wato Rahama Sadau sai ga Ali Nuhu yana bayanin cewa wai kungiyar na kokarin sassauta hukuncin da aka yanke mata

 - A wata tattaunawa da aka yi da sakataren kungiyar MOPPAN Salisu Mohammed ya ce, har yanzu Rahama Sadau korarriya ce daga finafinan hausa, ba kuma za ta dawo ba  

- Ko Ali Nuhu Yayi abin da ta yi a yanzu, za mu kore shi saboda jiya ba yau ba ce, bamu kuma tattauna da shi kan cewa za a dawo da Rahma ba

MOPPAN tace zata kori Ali Nuhu idan yayi laifi
Rahama Sadau da Ali Nuhu

Ali Nuhu da Rahama Sadau suna da ra’ayi daya a maimakon jarimi Ali Nuhu ya yaba da hukuncin da a ka yiwa Rahama Sadau, sai aka ji yana cewa, wannan hukuncin da a ka yi mata yayi tsauri, kwanaki kadan ya fito yana cewa, wai sun tattauna da Kungiyar MOPPAN cewa, za ta sassauta wannan hukunci.

Babban Sakataren kungiyar Salisu Muhammad, ya tabbatar da cewa, an koreta sannan ya kara da cewa, ba za a dawo da ita hakar wasan kwaikwayon ba,  Sakataren ya  kuma bayyana cewa, shima Ali Nuhu a cikin wasu finafinansa na baya yayi makamancin abin da ta yi na rungume-rungumen mata ko kuma sunbatarsu.

Ya ci gaba da cewa, ce babu abin da aka yi masa ne a sakamakon wannan kungiya ba ta da wasu tsare tsare da kuma hukunce-hukunce da suka yi hani da haka a waccan lokaci, amma idan ya ce zai yi abinda yayi a baya, to lallai za a koreshi kamar yadda a ka kori Rahama Sadau.

“Ali Nuhu yayi irin wadannan laifuka a shekaru biyu zuwa uku da suka wuce, a lokacin ba sabunta dokokin kungiya ba ne, ba kuma mu yi taron masu ruwa da tsaki ba ne, domin daga taron ne muka fitar da sabbin tsare-tsare da dokokin shirin fim.”

“A wannan taro Rahama ta na wurin, Ali Nihu kuma ya samu labarin abin da aka yi a taron. Amma tabbas ka sani idan Ali Nuhu ya sake irin abin da yayi a baya za mu kore shi kamar yadda muka kori Rahama Sadau a finafinan Hausa.”    

Asali: Legit.ng

Online view pixel