Yan wasan Arsenal sun caccaki Ozil

Yan wasan Arsenal sun caccaki Ozil

- Yan wasan koci Wenger sun yi wasa mai kayatar wa a gasar Champions Lig

- Ozil ya zura kwallaye guda uku

- Yan wasan Arsenal sun caccaki Ozil kuma sun fadi dalilin haka

Dan wasan tsakiya na kasar Germany ya jefa kwallo a wasar da Arsenal ta doke Ludogrets a gasar Champions Lig, amma abokan wasar shi na Arsenal sun caccaki shi.

Alexis Sanchez shi ya fara zura kwallo a ragar inda ya zura wata kwallo mai sha'awar kallo wadda Kila zata iya shiga a sahun kwallaye da zasu karbi kyauta a karshen gasar, sai Walcott da ta zura ta biyu, sai Chamberlain da ya jefa ta 3 bayan mintuna kadan daga dawowa hutun rabin lokaci, sai Ozil da jefa kwallaye 3 na karshe, inda Arsenal taci 6-0.

Yan wasan Arsenal sun caccaki Ozil
Mustafi da Ozil

KU KARANTA KUMA: Ogenyi Onazi ya maka tsohuwar kungiyar sa Lazio a katu

Bayan wasar sai Walcott yayi zolayar cewa "zan iya jefa shi kasan gada,a farkon lokacin wasa baya nan, ko kun gansh?

Mustafi dan wasar bayan Arsenal ya kara da cewa" wani lokaci nima yana zama man dole in caccake shi, haka kwallo take kowa yana yin kuskuren shi, amma dole mu yarda da haka a matsayin shahararrun yan wasa, amma wani lokaci dole mu caccaki kanmu,banda ma wadanda zasu caccake mu daga magoya bayan mu, kana son doka wasa, kana son cin nasara a wasa, baka son yin kuskure, in ma kayi kuskure kai zaka fara jin haushin kanka.

Ya kara da cewa" shi dan wasa ne mai kwazo, yana taimakon mu sosai, naji mai dadi na zura kwallo 3 da yayi na farko tun fara buga wasar shi.

Yana kokari, kowa yana yabon sa, dan yana taimaka ma yan wasan mu da yawa gurin zuwa kwallaye.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel