Ya musulunta saboda ya auri budurwarsa musulma

Ya musulunta saboda ya auri budurwarsa musulma

Wani Bature ya musulunta sakamakon soyayyar da yake yi ma budurwarsa musulma ma’aikaciyar wani kamfanin jirgin sama.

Ya musulunta saboda ya auri budurwarsa musulma

Shi dai mutumin ya hadu budurwatasa ce yayin daya shiga jirgin da take aiki a kan hanyarsa ta zuwa birnin Abu Dhabi daga garin Almaty na kasar Kazakstan. Tun bayan wannan haduwar ne soyayya ta kullu tsakanin Jeanne da saurayinta daya canza sunan sa zuwa Ibrahim.

An daura auren masoyan ne a kasaitaccen Otel dinnan mai suna Shangri-La dake kusa da babban masallacin Sheikh Zayed a birnin Abu Dhabi. Jeanne tace “mun samu kusan baki 200 daga kashe sama da 25 da suka halarci bikin namu. An daura auren mu kamar yadda musulunci ya tsara da safiyar ranar bikin.”

Ya musulunta saboda ya auri budurwarsa musulma

Mijina bature ne dan kasar Ingila, amma a dalilina ya musulunta. A kotun muslunci aka daura mana aure. Limamin masallacin ne ya daura mana aure a gaban iyayena da shaidu hudu, kuma an bamu takardan shaidan aure.”

KU KARANTA: Dokar kafa hukumar yankin Arewa maso gabas ya tabbata

Mun sanya hannun akan takardan yarjejeniyar aure, inda angon zai kawo shaidunsa akalla mutum biyu ko wakilinsa, tare da muharramin amarya su sanya hannu a kai. Daga nan sai angon da amarya su maimaita kalmar gamsuwa da auran juna na “Qabul” wato “na amsa” har sau uku.

Ya musulunta saboda ya auri budurwarsa musulma

Daga nan shikenan aure ya dauru sai a dan aka danyi kwaryakwaryan walima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel