Karamin yaro ya kera mota mai amfani da hasken rana

Karamin yaro ya kera mota mai amfani da hasken rana

Wani karamin yaro haziki mai tsananin basira daga jihar Ebonyi Ihere-serg Mascot ya kera wata mota dake amfani da hasken rana.

Karamin yaro ya kera mota mai amfani da hasken rana
Ihere-serg Mascot

Hazikin yaro Ihere-serg Mascot ya bayyana cewa motar tasa bata fitar da hayaki ko kadan, kuma bata amfani da man fetur.

Yaron ya samu daman nuna ma gwamnan jihar Ebonyi David Umahi motar tasa, yayin da ya kai mai ziyara a fadar gwamnatin jihar dake garin Abakal

KU KARANTA: Badakalar kudi:EFCC tana bincikar tsohon gwamna Chime

Yayin ziyaran gwamnan, Hazikin yaron ya tuka motar a gidan gwamnati inda ya zazzagaya a farafjiyar gidan, yayin da gwamna Umahi da sauran jama’a suka dinga sha’awar fasahar yaron.

Haka ma mutane da dama a shafukan sadarwa daban daban sun yaba da kokarin yaron, kuma sun bukaci gwamnatin jihar data taimake yaron wajen cimma burinsa.

Kalli hotunan motan:

Karamin yaro ya kera mota mai amfani da hasken rana
Mota mai amfani da hasken rana
Karamin yaro ya kera mota mai amfani da hasken rana
Yaron a cikin motarsa
Karamin yaro ya kera mota mai amfani da hasken rana
Gwamna Umahi tare da Yaron
Karamin yaro ya kera mota mai amfani da hasken rana

Ta wani hanya kuke gani ya kamata gwamnati ta taimaka ma yaron?

Asali: Legit.ng

Online view pixel