Daya daga cikin yaran Chibok da aka saki ta fadi inda sauran suke

Daya daga cikin yaran Chibok da aka saki ta fadi inda sauran suke

- 'Yan majalisar dattawa sun ziyarci yara 21 na Chibok wadanda 'yan Boko Haram suka sako

- Daya daga cikin 'yan matan chibok, Gloria ta roki sojojin Najeriya da kada su jefa bama-bamai a dajin sambisa don kada a kashe sauran yaran

Daya daga cikin yaran Chibok da aka saki ta fadi inda sauran suke
Yan matan Chibok da aka saka

Ya kamata dakarun yakin sama na Najeriya su daina jefa bama-bamai a dajin sambisa wanda yayi kaurin suna, kuma maboyar Boko Haram, cewar daya daga cikin yaran da aka sako. A cewarta, yaran dake tsare na cikin dajin, kuma ana iya kashe su maimakon 'yan ta'addar.

Gloria, daya daga cikin 'yan matan ta fada ma Ali Ndume, shugaba a majalisar dattawa yayin da ya ziyarci yaran da aka sako.

KU KARANTA: Matasa sun banka ma ofishin yan sanda wuta a Zamfara

Yace: "Lokacin da nike kan hanyar zuwa wajensu, ban san abinda zan gaya masu ba, amma bayan na isa sai suka rera mani waka. Ban san abin yi ba, sai na kare da kuka. Shugabarsu Gloria ita ta rika bani hakuri

"Ta ce in gaya ma sojojin sama su daina kai hare-hare a dajin sambisa domin gudun kashe sauran yaran. A mamadin Chibok, muna godiya gareku da duniya baki daya"

Asali: Legit.ng

Online view pixel