Ken Saro Wiwa ya Mutu

Ken Saro Wiwa ya Mutu

Mutanen yankin Niger Delta suna cikin jimami kasan cewar mutuwar Ken Saro Wiwa Jr da yayi.

Acewar sahara reportace, Ken SaroWiwa ya mutu ne ranar Talata 18 ga watan Oktoba.

Shidai yaro ne a wajen marigayi Ogoni, wanda ya taba zama mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara.

Haka kuma baban sa wato Ken Saro-Wiwo, yana daga cikin manyan mutane a garin Ogoni, sannan kuma daya ne daga cikin mutanen da akeji dasu a yankin Niger Delta gaba daya, sakamakon gudun mawarsa da yake baiwa mutanen yankin dangane da kasarsu da kuma gurbataccen ruwan da suke amfani dashi a yankin a sanadiyar kamfanonin mai dake yanki.

Ken Saro Wiwa ya Mutu
Ken Saro-Wiwa daya mutu

A shekarar 1992 an kulle Saro-Wiwa a gidan kaso na tsawon wasu watanni ba tare da wani dalili ba, karkashin mulkin soja. Haka kuma a watan yunin shekarar 1993, aka kara kamashi daga hukumomin gwamnati, inda bai cika wata daya ba aka kara sakin sa.

KU KARANTA KUMA: Tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi magana

Haka kuma an kara kama Saro-wiwa, inda ake zarginsa dasa hannu acikin kisan da akayima wasu manyan mutane guda 6 dake Ogoni, inda ya musanta zargin da akeyi masa, a inda ya kwashe shekara guda a gidan yari.

Daga baya ne aka gane yana da hannu dumu dumu acikin kisan, inda nan da nan aka yanke masa hukuncin kisa daga kotun turabunal.

A watan Nuwambar shekarar 1995, aka kashe shi tare da wasu mutane 8 da aka samesu da hannu a cikin kisan a lokacin mulkin jenar Sani Abacha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel