Horo! Uwa ta aske kan danta saboda halin sata da karya

Horo! Uwa ta aske kan danta saboda halin sata da karya

Gaskiyane, tsakanin uwa da da sai Allah, sau dayawa soyayya ke sanya iyaye horar da yayansu ba don basa sonsu ba.

Horo! Uwa ta aske kan danta saboda halin sata da karya

A haka ne wata mata dake garin Miami, na jihar Florida a kasar Amurka ta yi ma yaronta horo mai tsanani ta hanyar aske tsakiyar kansa saboda halin sata da yaron ke da.

Wanzamin daya aske kan yaron ne ya daura hoton a shafinsa na Facebook, inda ya nuna irin askin don ya kasance izina ga sauran yara.

Horo! Uwa ta aske kan danta saboda halin sata da karya

Shi dai wanzamin mai suna Steve ya rubuta a shafin Facebook “yau wata mata tazo tace in aske tsakyan kan yaronta mai shekaru 11, irin askin George Jefferson, saboda yana da halin sata da karya, yana satan mata kudi.”

KU KARANTA: Aisha Buhari sanye da rigar naira miliyan 1.2

Ni ko nace da wa Allah ya hada ni, in ba shi ba?" nan da nan na kwashe mai tsakiyan kai, kuma aka biyani, rib biyu"

Horo! Uwa ta aske kan danta saboda halin sata da karya
Horo! Uwa ta aske kan danta saboda halin sata da karya

Menene ra’ayinku game da wannan horon?

Asali: Legit.ng

Online view pixel