Matar da mijinta ya datse mata hannaye, ta samu na roba

Matar da mijinta ya datse mata hannaye, ta samu na roba

Yayin da wasu iyalai ke zaman jin dadi da juna, wasu kau cusa ma abokan zamansu bakin ciki da cutarwa kawai suke.

Matar da mijinta ya datse mata hannaye, ta samu na roba
Matar da mijinta ya dartse mata hannu

Da haka ne wata mata yar kasar Kenya ta shiga halin niyasu, bayan mijinta ya tafka mata wani rashin imani.

Ita dai wannan mata mai suna Jackline Mwende ta shiga tasko ne yayin da mijinta yayi mata dukan kawo wuka, ya jijji mata ciwuka a fuska, tare da barin mata tabo iri iri, kai daga karshe ma sai ya datse mata hannaye!

Matar da mijinta ya datse mata hannaye, ta samu na roba

Kash! Wai Duniya ina zaki damu?

Rahotannin sun nuna wai mijin yace ya horar da ita ne sakamakon rashin haihuwa, a lokacin da wannan mummunar labara ya bayyana, al’ummar kasa Kenya sunyi matukar kaduwa, sai dai sun kawo matar dauki.

KU KARANTA: Sojoji sun kama babban kwamandan tsagerun Neja Delta

Nan da nan aka samu wasu bayin Allah suka jikan Mwende, inda suka garzaya da ita kasar Korea ta kudu, a can ne ta samu kulawa daga kwararrun likitoci, wadanda suka sanya mata hannayen roba.

Ana sa ran idan ta warke yadda ake tunani, zata samu damar gudanar da kasha 80 na ayyukan da hannu na gaske ke iya yi.

Ga yadda warakar nata ke kasancewa.

Matar da mijinta ya datse mata hannaye, ta samu na roba
Matar ta warke sanye da hannayen roba

Asali: Legit.ng

Online view pixel