Gwarzon duniya Lionel Messi ba lafiya

Gwarzon duniya Lionel Messi ba lafiya

Kwanan ne dai dan wasan kwallon kafa na duniya Lionel Messi ya samu sauki daga wani ciwo da yayi

Sai kuma ga Dan wasa Lionel Messi yana ta amai yayin da ake buga wasa

– Hankalin Magoya bayan dan wasan na duniya ya tashi

Gwarzon duniya Lionel Messi ba lafiya
Lionel Messi yana kwarara amai

Dan wasan kwallon kafa na duniya, Lionel Messi ya samu sauki daga wani ciwo da yayi, bayan yayi jinya na ‘yan makonni. A karshen wannan makon ne dan wasan na Kungiyar Barcelona ya dawo cikin fili domin wasa.

Yayin da dan wasa Lionel Messi yake zaune bisa benci sai kawai aka ya buge da amai, wannan abu ya tada hankalin jama’a da dama ainun, hankalin Magoya bayan dan wasan na duniya ya tashi kwarai da suka gan sa a wannan yanayi

KU KARANTA: Ina nan a raye Inji mai mata 86

Sai dai dan wasan na duniya Lionel Messi yace wannan ba wani abin a tada hankali bane, domin kuwa ya saba irin wannan amai. Lionel Messi yace: ‘Wannan amai ai ba wani abu bakon abu bane, yak an faru sau da dama, a nan Barcelona na sha yin hakan, saboda haka babu wani abin damuwa’

Duk da wannan abu da ya faru lokacin da dan wasan ke kokarin shigowa wasa, dan wasa Lionel Messi na shigowa cikin fili ya zura kwallo ko minti biyar ba ayi ba. Barcelona ta doke Kungiyar Deportivo da ci uku da nema a wasan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel