Rotimi Amaechi ya musanya zargin Alkali

Rotimi Amaechi ya musanya zargin Alkali

Ministan Sufuri na Tarayya ya musanya zargin Alkalin Kotun Koli John Okoro

Rotimi Amaechi yace karya Alkali Okoro yake masa, bai taba zuwa wajen sa ba

– Alkalin yace ana binciken sa ne domin ya ki yi wa su Rotimi Amaechi da APC aiki

Rotimi Amaechi ya musanya zargin Alkali
Rotimi Ameachi tare da shugaba Muhammadu Buhari

Ministan Sufuri na Tarayyar Kasar nan Mista Rotimi Amaechi ya musanya zargin Alkali John Inyang Okoro na Kotun Koli. Rotimi Amaechi yace karyar banza ce Alkalin ya sheka, kuma maganar sa babu kanshin ko gaskiya a cikin ta.

John Inyang Okoro na Kotun Kolin Kasar, ya rubuta takarda ga Shugaban Alkalan Kasar inda yace an kama sa ne don bai yi wa Jam’iyyar APC da su Muhammadu Buhari aiki ba. Alkalin yace Minista Rotimi Amaechi yayi kokarin neman sa da ya canza hukuncin zaben Jihar Rivers, Abia da kuma Akwa-Ibom.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai yaki rashawa gadan-gadan

A wata takarda kuwa da shi Ministan Tarayyar, Rotimi Amaechi ya rubuta, ya musanya duk wannan zargi. Rotimi Amaechi yace Alkalin ya kirkiri wannan karyayyaki ne daga tunanin sa, yake cewa babu kanshin gaskiya a cikin wannan magana ko kadan Rotimi Amaechi yace ko hankali ma ba zai dauki hakan ba.

Rotimi Amaechi yace Alkali John Inyang Okoro kokarin siyasantar da Binciken na sa da Hukumar DSS. Ministan yace Alkalin yayi ta kan sa, kar ya sanya sa a ciki. Ba nan kadai ba Rotimi Amaechi yace ba zai bar wannan magana ba, sai ya kai Kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel