Jibril ya tona asirin yadda yan majalisa ke kashe kudi

Jibril ya tona asirin yadda yan majalisa ke kashe kudi

- Abdulmumin Jibril ya zargi kakakin majalisa da sauran yan majalisa kan satar kudin kasa.                                                     

- Dan majalisar yace ana zargin yan majalisar da kashe kudin kasa gurin hayar gidajen hutawa.                                               

- jibril yace duk yan majalisar abunda suke yi a gidan hutawar su shine suyi biki na karya da sharholiya da karywai.

Tsohon shugaban kwamitin dai-daito na kassafi, Abdulmumin Jibril ya bayyana cewa da kakakin majalisa da mataimakin kakakin majalisa da Yusuf Suleman Lasun da sauran mambobin majalisa, sun dauki shekaru suna dibar kudi daga asusun gwamnati da yin biki da sharholiya da karuwan su a gidajen su da suke haya na hutawa.

Jibril ya tona asirin yadda yan majalisa ke kashe kudi
Abdulmumin Jubrin da Yakubu Dogara

Jibril yana zargin Dogara da sauran yan majalisa kan yin abubuwan da basu dace da su ba.

KU KARANTA KUMA: Anci mutuncin sarauniyar kyau

Dan majalisar mai wakiltar Kiru/Bebeji ta jahar Kano a majalisar tarayya, ya bayyana cewa Dogara da Lasun sun karbi miliyan N500 daga gurare da dama dan ansar hayar gida duk da sunan" basu samu gidajen da gwamnati ke bada wa ba".

Jibril yayi zargin a shafinsa na twitter, inda yake cewa har lokacin da kasar nan suke cikin babu, yan majalisa suna satar kudin kasa, suna cinye ma talakawa wahalar su.

Yan majalisa suna satar biliyoyin kudi dan kama gidan hutawa su aje jaruwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel