An dakatar da karatun difloma a jami'oin Najeriya

An dakatar da karatun difloma a jami'oin Najeriya

- Hukumar da ke sa ido kan jami'oi ta Najeriya, NUC, ta haramta karatun diploma da jami'o'in kasar nan ke bayarwa.

- Hukumar ta ce duk da cewa jami'o'in sun kwashe shekara da shekaru suna yin hakan a wurinta sun sabawa ka'ida kuma karatun haramtacce ne.

An dakatar da karatun difloma a jami'oin Najeriya

Guraben karatu da jami'oin gwamnatin kasar ke samarwa dai sun yi karanci ga miliyoyin mutanen da ke bukatar karatu mai zurfi a kasar duk kuwa da cewa an samu yawaitar jami'o'i masu zaman kansu fiye da a baya a kasar.

Daraktan hulda da jama'a na hukumar ta NUC, Malam Ibrahim Usman Yakasai, ya gaya wa manema labarai cewa, in ban da difloma da ake yi a jami'ar ABU, tun lokacin Frimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello, Sardauna, ba a yarda da duk ta wata jami'a ba.

Jami'in ya ce duk dalibin da yake son yin karatun difloma sai ya je kwalejojin kimiyya da fasaha (polytechnics),amma ba jami'a ba.

KU KARANTA KUMA: Wani mummunan rikici ya sake kunno kai a jihar Kaduna

A wani labarin kuma Shugaban kwamitin ba fadar shugaban kasa shawara a kan yaki da cin hanci da rashawa, Itse Sagay ya bayyana cewa da ba shugaban kasa Buhari ba shi ke kan shuganan cin kasar nan a yanzun ba da tuni kasar ta zo karshe.

" da Buhari bai zo ba, ba na tunanin da har yanzun akwai wata kasa Nijeriya" Da sai kasar Zimbabwe ta fi Nijeriya inji Mr Sagay.

Sai dai dinbi masu maida martani a kafar da muka samo labarin ta Premium Times , dumbin masu mayar da musayar ra'ayi na ta sukar lamirin maganar ta Mr Itse Sagay, inda suke cewa a ciki maganar tasa ya mance Allah ya sa shugaba Buhari a matsayin danda ya tsare kasar ba Allah ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel