Nigerian news All categories All tags
Alkalai biyu sun sha tambayoyi a hannun hukumar EFCC

Alkalai biyu sun sha tambayoyi a hannun hukumar EFCC

Hukumar yaki da zamba da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta fara matsar wasu alkalan da take zargi da karbar cin hanci da rashawa a kasar nan.

Alkalai biyu sun sha tambayoyi a hannun hukumar EFCC

Alkalan yayin isarsu ofishin hukumar EFCC

Vanguard ta ruwaito wasu alkalan babban kotun tarayya, Mohammed Nasir Yunusa da Hyeladzira Ajiya Nganjiwa da ake zargi da hannu dumu-dumu cikin aikata cin hanci da rashawa sun gurfana a gaban ofishin hukumar EFCC dake jihar Legas domin amsa tambayoyi.

A yan kwanakin nan ne hukumar tsaro ta sirri (DSS) ta kama wasu alkalai a gidajensu, sai dai kungiyar alkalan kasar nan (NJC) tayi tir da kamen.

KU KARANTA: Ya cizge kunnen makwabcinsa kan bishiyan ayaban-suya

Yayin da NJC da NBA suke sukar lamirin hukumar DSS, shi ko shugaban kasa Muhammadu Buhari jiyo shi aka yi yana nanata manufar sa na hukunta duk wanda aka kama da laifin aikata cin hanci da rashawa.

Vanguard ta ruwaito cewa da misalin karfe 10:05 na safe ne alkalan suka hallara ofishin, inda ba’ayi wata wata ba aka shigar dasu dakin bincike.

Wata majiya inji rahoton tace “an gayyace su ne sakamakon zargin karbar cin hanci da aikata almundahanar kudi da hukumar EFCC ta gano yayin binciken wasu lauyoyi guda biyu wanda yanzu haka suna gaban kuliya.” Majiyar ya kara da cewa “a yanzu haka alkalan suna bamu hadin kai wajen amsa tambayoyin mu.”

A ranar lahadi 16 ga watan Oktoba ne dai Legit.ng ta buga sunayen alkalan da aka mika ma shugaba Buhari wadanda ake zargi da aikata almundahanar kudi.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel