Aisha Buhari da sauran kalamai

Aisha Buhari da sauran kalamai

Najeriya ta shiga ruguntsimi a wannan mako a sakamakon furucin matar shugaban kasa da ya jano ka-ce-na-ce, da ma wasu kalamai na ‘yan kasar dangane da abubuwan da suke faruwa.

Aisha Buhari da sauran kalamai
Uwargidan shugaba Buhari

“ ‘Yar manuniya ce ta nuna cewa lalllai ‘yan adawa na amfani da ita wajen yiwa gwamnati zagon kasa. Kuma kalamanta ba su dace ba, kuma za su iya haddasa tashin hankali”.   

Wani malamin Islama Sheikh Ilyasu Mangu a kirarasa ga jami’an tsaro da su kama matar shugaban kasa bisa kalamanta a hirarta da BBC.

Aisha Buhari da sauran kalamai
Aisha Buhari

“Ba zan sake fita yawan neman kuri’a ba tare da kiran mata su yi zabe kamar yadda na yi a da ba. Dan ba kara”

Matar shugaban kasa na garagadin mijinta cewa, ba za ta sake mara mi shi baya a zabe na gaba ba, idan har bai yiwa gwamnatinsa garanbawul ba.

Aisha Buhari da sauran kalamai
Buhari tare da uwargidansa Aisha

“Ban san jam’iyyar da matata ta ke ba, amma dai na san cewa, ita ke kula da dakin dafa abincina da falo na da kuma turakata”  

Martanin shugaba Buhari cikin raha ga kalaman matarsa na cewa ba za ta sake mara masa baya ba.

Aisha Buhari da sauran kalamai
Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose yace yana fatan kada abunda ya faru da Safina ya faru da Aisha

“Ina dai fatan cewa Aisha ba za ta sha wahalar da Sefinatu ta sha a wurin Buhari ba”  

Ayo Fayose na sharhi kan kalaman Aisha Buhari dangane da hirarata da BBC

Aisha Buhari da sauran kalamai

“Da akwai wani kulinboto da siddabaru a fadar mulkin Nigeria da ke tasiri a kan gwamnati”

Tsohon kakakin shugaba Jonathan Reuben Abati a banyaninsa na wasu abubuwa da ke faruwa a fadar mulkin kasar ta Aso Rock

Aisha Buhari da sauran kalamai
Tsohon shugaban kasa Obasanjo

“Yanzu ta fito karara cewa ya kwafsa a baya. Ba mutumin da za a amincewa ba ne”  

A ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, bayan da aka sako ‘yan matan Chibok 21 ke sukar furin shugaba Buhari wanda ya yi a baya kan cewa, ba za a taba gano ‘yan matan ba.

Aisha Buhari da sauran kalamai

“Yayin da kowa ke kyamar cin hanci da rashawa muke cewa, ya ya kamata a bi tsari sanin yakmata a harakara kudi”

Furucin gwaman Ayo Fayuose na jihar Ekiti a lokacin da yak e bayyana ra’ayinsa ga labarain sakin ‘yan matan Chibok da cewa dabarar dauke hankulan ‘yan kasa ne daga halin yunwa da suke fama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel