Sau 4 Mourinho yana fadin magana mara dadi a kan Liverpool

Sau 4 Mourinho yana fadin magana mara dadi a kan Liverpool

Kan wasan da za'a doka tsakanin kungiyar Liverpool da Manchester United, munyi duba kan maganganu 4 da Mourinho yayi mara dadi akan Liverpool. 

Ba wani tsohon labari ba ne inda Mourinho ya nuna yana son ya horar da kungiyar Liverpool a shekara ta 2004, kafin a ba Rafael Benetiz wanda ya taimaka ma kungiyar taci Champions Lig a shekara ta 2005.

Sau 4 Mourinho yana fadin magana mara dadi a kan Liverpool

Jose Mourinho ya boye kwallo daga Steven Gerrard a wasar da Chelsea ta doka da Liverpool a gasar firimiya Lig ta 2014.

Duk da kaunar da yake ma kungiyar Liverpool, be sa ya dauki sauki ga Benetiz ba da ita kanta kungiyar, ga maganganu guda 4 nan da muka dauko yayi akan kungiyar ta Liverpool.

1. Bayan wasar da yayi da Liverpool a 2005 wadda Luis Garcia yaci.

Yace anci kungiya kwararra, bayan sunci, mu kawai muka fito muka yi wasa, su sun tsare gida ne.

2. Yawan cin ma'aikatan gidan talabijin na wasanni yan Liverpool be.

Carragher Liverpool,  Thompson liverpool, Redknapp Liverpool, Hensen Liverpool, Lawrenson Liverpool, ba kowa daga Chelsea, bayan nayi ritaya a lokacin ina da shekara 75 zanje in kare Chelsea.

3. Yace Liverpool ba babban kungiya bace kafin buga wasar kusa da ta karshe a shekara ta 2007 .

Tarihi ze mai mata kanshi, a tarihi ma Liverpool ba wata babbar kungiya ba ce, amma in zaku iya tunawa a shekarun baya sun buga gasa 1 kacal, kuma sun fita da wuri.

Kuma kungiyar mu ta Chelsea zata ba Liverpool maki 60.

4. A lokacin da ya bata ma Barden duk kokarin da yayi na cin firimiya Lig.

Ina ji wannan ranar itace ranar da Liverpool zasu tafi dan cin kofi, zamu je dan mu zama abun dariya, na fada ma yan wasa na da ba zamu taba zama abun dariya ba.

Wace kungiya kuce tunanin zasu nasara a wasar yau?

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel