Hukumar EFCC na binciken Ministocin Najeriya

Hukumar EFCC na binciken Ministocin Najeriya

An samu labarin cewa Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa na binciken wasu daga cikin Ministocin Buhari

Binciken dai yana da alaka da wasu makudan kudi da aka sace a baya

Sai dai Hukumar EFCC din tayi bakkam game da wannan maganar

Hukumar EFCC na binciken Ministocin Najeriya
Jami'an Hukumar EFCC

Rahotanni sun nuna cewa Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta budo shafin wasu daga cikin Ministocin Najeriya domin bincike. Duk da dai ana maganar cewa lambar wasu daga cikin Ministocin ya fito, har yanzu dai Hukumar EFCC ba ta gayyace su ba domin amsa tuhuma.

Rahotannin sun nuna cewa ana binciken wasu Ministoci ne daga Kudancin Kasar, binciken dai yana da nasaba da batar da wasu Miliyoyin kudi da Ministocin suka yi a wani lokaci. Duk da dai ba a bayyana sunan Ministocin ba, sai dai an bayyana irin badakalar da suke aikatawa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sha alwashin kama duk wani barawo

Jaridar Punch ta ce Hukumar EFCC na binciken wani daga cikin Ministocin ne game da bada lasisin Soji a Ma’aikatar sa, wanda hakan ya jawo masa makudan kudi na Biliyoyin Naira. Daya daga cikin Ministocin kuma yana da hannun-jari ne a wani Kamfanin sadarwa, wanda yake amfani da shi wajen satar kudi zuwa wajen Kasar.

Da alamu dai cewa ana kan binciken har yanzu, sai dai Jami’in watsa labarai na Hukumar EFCC Wilson Uwajaren yace shi fa bai san da maganar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel