Tsageru: Za mu saka kafar wanda daya da ku-Sojin Ruwa

Tsageru: Za mu saka kafar wanda daya da ku-Sojin Ruwa

Rundunar Sojin ruwan Najeriya sun gargadi Tsagerun Neja-Delta

Sojin ruwa na Najeriya sun ce idan har Tsagerun suka kara taba butatan man Kasar za su ga abin da zai faru

Kungiyar Tsagerun NDGJM sun yi barna kwanan nan

Tsageru: Za mu saka kafar wanda daya da ku-Sojin Ruwa
Sojin ruwa

A kwanan ne Kungiyar Tsagerun NDGJM watau Niger Delta Greeland Justice Mandate suka kai hari a wani bututun man Kamfanin mai watau NNPC na Kasar. Tun kwanaki dai Kungiyar ta Niger Delta Greeland Justice Mandate ta saba irin wannan barna.

Don haka Rundunar Sojin ruwa na Kasar ta gargadi Tsagerun da su guji aikata irin haka a gaba. Rundunar Sojin ruwa tace za ta koyawa Tsagerun hankali idan har bas u guji irin wannan barnar ba. Sojin ruwa sun yi alkwarin damke duk wani tsagera sannan kuma a hukunta sa.

KU KARANTA: Matan Chibok: Rundunar Soji tayi magana

Wani kwamandan Rundunar Sojin ruwa Commodore Habib Usman ya bayyana haka ne lokacin da Rundunar sa suka ba da magani kyauta ga mutanen yankin Akenpai da ke Yenegoa. Commodore Habib Usman yace wasu masu tada kafar baya ne ke kokarin hada fada Gwamnati da mabiya.

Kwamanda Habib Usman yace tabbas idan tsagerun ba su bi a hankali ba, kwanan za a ga bayan su. Rundunar Sojin ruwa sun nemi hadin kan al’umma domin kama masu tada zaune tsayen. Rundunar Sojin ruwa ta bayyana cewa yanzu fa duk wanda aka kama, kar ya ga laifin kowa sai Karen kan sa.

Ku kalli wani bidiyo:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel