Wasu makiyaya da ake zargi sun kaima wasu 'yan sanda hari,

Wasu makiyaya da ake zargi sun kaima wasu 'yan sanda hari,

- Wasu yan bindiga dadi wa'anda ba'a san ko suwa nene ba sun kashe 'yan sanda guda biyu a wurin da ake ababan hawa a hanyar kagoro gidan waya a jahar Kaduna, wanda ake tsammanin Fulani makiyaya ne suka aikata abin

- Haka kuma, 'yan bindigan sun kaima 'yan sandan harsu shida farmaki, wa'anda suke kula da motocin dake zirga-zirga a hanyar, a inda suka kashe 'yan sandan guda biyu, sauran kuma sukaji mummunar rauni

- Har ila yau kuma, 'yan bindigan sun gudu da bindigu guda biyu kirar AK47 tare da harsashen ta wanda suka kwace a hannun 'yan sandan

Wasu makiyaya da ake zargi sun kaima wasu 'yan sanda hari,

An kashe wasu 'yan sanda guda biyu ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba a inda ake duba ababan sufuri akan hanyar kagoro gidan waya a karamar hukumar Kaura a jahar Kaduna. Inda ake zargin Fulani ne makiyaya suka aikata al'amarin.

Acewar Daily Trust, makiyayan sun farma 'yan sandan ne harsu shida a lokacin da suke duba ababan sufuri, inda suka kashe mutane biyu nan take, sannan kuma sauran sukaji mummunar rauni.

Haka kuma, biyu daga cikin 'yan sanda guda shindan sun tsira da kyar inda babu abinda ya same su.

Sannan kuma andai bayyana cewar, 'yan bindigan sun gudu da bindigun su kirar AK47 guda biyu, tare da harsashe su.

'Yan sandan da suka mutu, suna da mukamin sajent, a inda aka kaisu yankin domin su lura da matsalar da yankin take fama dashi na kashe-kashen mutane da akeyi a yankin.

Wani mutum wanda ake cema Enoch Andong, wanda a unguwar yake, wanda ya taimaka aka dauki gawarwakin 'yan sandan guda biyu da suka mutu zuwa babban asibitin dake garin Kafanchan, ya bayyana cewar lamarin dai ya farune da misalin karfe 9:30 na safe, inda fulanin sukazo suga budema 'yan sandan wuta.

Haka kuma, sarkin musulmi na Sokoto, Sultan Abubakar Sa'ad, ya bayyana cewar a kama fulani makiyaya dake harkar ta'addanci a duk inda suke a fadin kasar nan, a ranar Litinin 10 ga watan Oktoba.

Haka kuma, wasu Fulani sun nisanta kansu da harkar ta'addanci, inda sukayi tir da Allah wadai da irin wannan dabi'ar. Inda sukace waisu sunayi ne da sunan musulinci, alhali musulinci baice a kashe mutum ba baijiba kuma bai gani ba. Saboda haka wannan abinda sukeyi bada yawun musulman Najeriya sukeyi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel