Manyan Igbo suka gurgunta Biafra - Uwazuruike

Manyan Igbo suka gurgunta Biafra - Uwazuruike

- Basarake Ralph Uwazuruike ya zargi manyan Igbo kan cin Biafra da yaki da kuma maida su bayi da gwamnati keyi a Najeriya

- Shugaban MASSOB din yace masu zagon kasa maimakon su kare 'yan uwansu Igbo, suna hada kai da makiyansu domin cutar da Igbos

- Uwazuruike yace matsalar Ndigbo tafi karfin maida su saniyar ware da akeyi, ya nace kan 'yancin kai daga Najeriya

Manyan Igbo suka gurgunta Biafra - Uwazuruike
MASSOB

Shugaban kungiyar neman 'yancin Biafra (MASSOB), basarake Ralph Uwazuruike ya danganta cin Biafra da yaki da akayi kan manyan Igbo wadanda ya kira masu zagon kasa.

KU KARANTA: An banka ma barayin waya wuta a Abuja

Uwazuruike, ya fadi haka ta wani jawabi daga bakin daraktan watsa labarai na wani gangamin masu neman 'yancin Biafra koko Biafra Independence (BIM), Mazi Chris Mocha, wanda ke cewa zagon kasa daga manyan Igbos ya jaza cinsu da yaki da kuma yadda gwamnatin Najeriya take maida Ndigbo bayi.

A cewar Vanguard, shugaban MASSOB din yana jin takaicin hada kan da masu zagon kasa keyi na cutar da 'yan uwansu Igbo maimakon kare su, suna kuma kiran kansu shuwagabannin Igbos. Yace abubuwan da suka jaza kafa MASSOB wadda ta zama BIM ke nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel